Home Ilimi WAEC ta ƙara kuɗin jarrabawa zuwa N18,000

WAEC ta ƙara kuɗin jarrabawa zuwa N18,000

0
WAEC ta ƙara kuɗin jarrabawa zuwa N18,000

 

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandare ta Afirka, WAEC ta sanar da ƙarin kuɗin jarrabawar kammala makarantar sakandare, WASSCE, inda ta ƙara N4,050 a kan kowanne ɗalibi.
Hukumar ta sanar da cewa ta ƙara kuɗin jarrabawar ne da ga N13,950 zuwa N18,000, amma daga baɗi ƙarin zai fara.
Shugaban babban Ofishin Hukumar na Ƙasa, Patrick Areghan ne ya baiyana hakan yayin da ya ke sanar da sakamakon jarrabawar WASSCE ta 2021 ga ɗalibai a ranar Litinin a Jihar Lagos.
Areghan ya alaƙanta ƙarin farashin jarrabawar da tashin farashin kayaiyaki a ƙasar, wanda annobar korona ta haifar.
“Kamar yadda hauhawar farashin kayaiyaki ya ke kassara harkoki a ƙasar nan kuma muma kuɗin gudanar da Jarrabawar nan ya ƙaru sosai, a gaskiya ba za mu iya shirya jarrabawar a kan N13,950 ga kowanne ɗalibi ba.
“Diba da haka mun samu sahalewa daga mahukunta cewa daga WASSCE ta shekarar 2022 za a fara karɓar N18,000 daga kowanne ɗalibi da zai zana jarabawar.
“Sabo da haka muna kira ga duk shugabannin makarantun sakandare a faɗin ƙasar nan da su karɓi N18,000 da ga kowanne ɗalibi,” in ji Areghan.