Home Kasuwanci Wahalar man dizel: Dole sai mun ƙara farashin yashi, dutse da ƙasa — Ƴan tifa

Wahalar man dizel: Dole sai mun ƙara farashin yashi, dutse da ƙasa — Ƴan tifa

0
Wahalar man dizel: Dole sai mun ƙara farashin yashi, dutse da ƙasa — Ƴan tifa

 

 

Ƙungiyar Direbobin Tifa ta ce ya zama dole ta ƙara farashin yashi, dutse, ƙasa da sauran kayan gini, sakamakon tashin farashi da kuma wahala ta man dizel.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa motocin ɗiban yashi, wanda a hausance a ke kiran su da tifa, da man dizel su ke amfani ba man fetur ba.

Tuni man dizel dai ya yi tashin gwauron zabi da ga N400 zuwa N670 lita ɗaya, inda kuma ya yi wahalar samu a ƙasar.

Shugaban Kungiyar Direbobin Tifa ɗin, reshen Jihar Kano, Mamuna Ibrahim Takai ya ce babu yadda za a yi sai an yi ƙarin farashin, in ba haka ba, sai dai su tsaya da harkar ta su.

A cewar sa, farashin man dizel ya tashi, idan ba su ƙara farashin kayaiyakinsu ba, to za su riƙa ƙirga faduwa ne, a maimakon riba.

Ya ce mataki ne mai wuya amma dole a yi haƙuri a karɓa sabo da yanayi ne ya haifar da hakan.

“Za a samu karin farashin yashi da dutse. Abu ne da ba a son ran mu ba. In ba haka ba sai dai mu rufe kasuwancin namu mu jira lokacin da zai sakko. A yi hakuri, yanayi ne ya haifar da hakan”, in ji shi.