
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci Hukumar Samar da Ruwan sha da Tsaftar Muhalli, RUWASSA da ta gaggauta gyara rijiyoyin burtsatse da su ka lalace a Ƙananan Hukumomi takwas na cikin ƙwaryar Kano, a wani mataki na magance matsalar ruwan sha a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abba Anwar, Babban Sakataren yada Labarai na gwamna Abdullahi Ganduje ya fitar a jiya Lahadi a Kano.
Ya ce, Ganduje ya ba da umarnin ne a wani taro da jami’an Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jiha, RUWASSA da kuma Shugabannin Ƙananan Hukumomi takwas na jihar.
Gwamna Ganduje ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf-Gawuna a wajen taron.
Anwar ya ambato Ganduje ya na cewa, “Ya kamata RUWASSA ta kuma dauki jerin sunaye, musamman a kananan hukumomi 44 da ke bukatar rijiyoyin burtsatse, tare da la’akari da matsalolin da yawaitar rojiyoyin burtsatse ke haifar wa ga muhalli”.
Gwamnan ya kuma umurci kansilolin manyan biranen jihar da su yi amfani da tankunan ruwa don raba ruwa ga mazauna yankunan a wurare masu mahimmanci, a matsayin mafita cikin gaggawa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta karfafa hadin gwiwa da hukumar raya kasar Faransa domin samar da mafita na tsawon lokaci don inganta samar da ruwan sha a jihar.
Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta kara kaimi wajen karfafa tsaro a kewayen kayan aikin ruwa.
“Kuma duk wanda aka samu yana so zai fuskanci fushin Shari’a. Muna yin dabarun kan hakan da gaske.
“Gwamnati tana tsara hanyoyin samar da na’urorin ruwa masu nauyi, injina masu karfin wuta, sarrafa satar waya da sauransu.
“Muna tabbatar wa mutanenmu cewa abin da muke da shi a kan tebur, shi ne na gajeren lokaci, tsakiyar wa’adi da kuma dogon lokaci,” in ji shi.