
Kocin tawogar ƙwallon ƙafar Netherlands, Louis Van Gaal ya kafe kan cewa shi fa ƙwaƙwalwarsa garau ta ke bayan ya samu haɗari a kan keke wanda ya koma yawo a keken-guragu.
Van Gaal ɗin ya faɗi ne a kan keke a ranar Lahadi in da ya bugu a ƙugunsa, amma ya ja tawogar zuwa attisaye a ranar Litinin domin wasan share fagen shiga gasar kofin duniya da ƙasar Norway.
Van Gaal, wanda shi zai ja ragamar ƙasar ta sa su kara da Norway a Rotterdam, ya nanata cewa shi fa ƙwaƙwalwarsa garau ta ke duk da haɗarin da ya yi.
“Duk da cewa na bugu a jiki na, amma ƙwaƙwalwa ta ta na aiki daidai, in ji tsohon kocin Manchester United da Barcelona.
Da a ka tambaye shi ko da zafi?, ai kuwa sai ya kada baki ya ce “gaskiya da zafi. Na ɗanɗana kuɗa ta. Shi ya sa ma ku ka ganni a kan keke guragu.”
“Amma kuma ba abin da ba zan iya ba saboda ƙwaƙwalwa ta ta na aiki yadda ya kamata,”