Home Lafiya WAMY, gwamnatin Jigawa, gidauniyar Malam Inuwa za su yi aikin ido kyauta ga al’umma

WAMY, gwamnatin Jigawa, gidauniyar Malam Inuwa za su yi aikin ido kyauta ga al’umma

0
WAMY, gwamnatin Jigawa, gidauniyar Malam Inuwa za su yi aikin ido kyauta ga al’umma

 

Ƙungiyar Matasa Musulmi Ta Duniya, wacce a turance a ke kiran ta da World Assembly Of Muslim Youth, WAMY, da haɗin gwiwar gwamnatin jihar jigawa, da gidauniyar malam inuwa za su yi aikin ido kyauta ga al’ummar jihar.

Wata sanarwa da kwamitin gudanarwa na Gidauniyar Malam Inuwa ya fitar a yau Juma’a ta baiyana cewa za a yi wa masu matsalolin ido aiki ne kyauta ga ɗaukacin al’ummar Jigawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin ya ƙunshi duba marasa lafiyar idanu, yi musu aiki, basu magani da gilashi kyauta.

Ta kuma sanar da cewa za a gudanar da gagarumin aikin a ranar Lahadi zuwa Laraba dai-dai da 16 zuwa 19 ga watan rabiu thani, wanda ya yi daidai da 21 zuwa 24 ga wata nuwamba.

Sanarwar ta baiyana cewa za a yi aikin ne a babban asibitin Hadejia, Jihar Jigawa.

“wannan aiki ya shafi al’ummar jihar jigawa ne baki ɗaya,” in ji sanarwar.