
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta tabbatar wa ƴan ƙasar cewa ba za a iya yin kutse cikin na’urar tattara sakamakon zaɓe domin sauya bayanan da ke cikin na’urorin ba.
Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani, Lawrence Bayode ne ya tabbatar da haka a wata hira da gidan Talbijin din Channels TV a yau Laraba .
Ya ce ba za a iya yi wa na’urar kutse a ranar zaɓe ba.
”Ina so in sake tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa ba a yi wa na’urar kutse ba, za a kiyaye duka bayanan da ke cikin na’urar”.
“Bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na’urarmu, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na’urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su”, in ji shi
Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na’urorin ba.