
Wata sabuwar rigima na shirin kunno kai s jam’iyyar PDP kan barazanar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi na ficewa daga yakin neman zaben Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Mohammed ya fusata ne kan wasu bayanan sirri da ya samu na cewa Atiku ba ya son tikitin tsayawa takarar gwamna karo na biyu da ya samu a Bauchi.
Gwamnan ya yi zargin cewa Atikun ba ya bashi dama ya bada gudunmawarsa wajen gudanar da yakin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa a Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya kuma koka da yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya raina shi.
Ya ce a cikin dukkan masu neman takarar shugaban kasa a PDP, shi kadai ne Atiku bai kai wa ziyara ba domin sasantawa da sulhu.
An tattaro cewa Mohammed ya zabi ya fice daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP din ne, duk da nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin shugaban yankin na Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya yi zargin cewa tun da dan takarar bai aminta da shi ba, zai so ya tsaya a waje ɗaya ya zura ido.
Amma kuma shugaban jam’iyyar, Iyochia Ayu ya jagoranci wata tawaga zuwa jihar Bauchi a ranar Asabar don sasanta lamarin.
Tawagar wacce ta hada da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, sun yi alkawarin duba batutuwan da suka taso domin sulhunta wa.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da kuma a jiya, gwamnoni biyar da suka fusata – Nyesom Wike (Rivers), Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Samuel Ortom (Benue) da Seyi Makinde (Oyo) – sun yanke shawarar ci gaba da yakin su da Atiku da shugaban kasa Iyorchia Ayu.