Home Labarai Wani Mutum da matarsa ke yawan yi masa gorin bashi bane uban ‘ya’yansa ya kashe yaran 4 da kanwar matar

Wani Mutum da matarsa ke yawan yi masa gorin bashi bane uban ‘ya’yansa ya kashe yaran 4 da kanwar matar

0
Wani Mutum da matarsa ke yawan yi masa gorin bashi bane uban ‘ya’yansa ya kashe yaran 4 da kanwar matar

 

Hassan Y.A. Malik

Wani mutum mai matsakaicin shekaru da aka bayyanasa da Stephen Nnadiogo, wanda ke zaune a gida mai lamba 21B, kan titin Ntueke, unguwar Awada Obosi, cikin karamar hukumar Idemili ta arewa da ke jihar Anambara, ya kashe yaransa 4 da kanwar mai dakinsa da mai dakin nasa sakamakon zargin mai dakinsa da ya ke yi da neman maza.

Yaran wadanda 2 maza ne 2 kuma mata sun gamu da fushin mahaifinsu da rahotanni suka ce ya gaji da gorin da mai dakinsa ke yi masa na cewa yaran da ya raina a matsayin ‘ya’yansa ba nasa bane na wasu maza ne a waje.

Matar ta Stephen kan kara da kiransa da juya wanda ba ya iya tsinana wani abin kirki ta fuskar mu’amalar aure kuma ba zai iya haihuwa ba, dalilin da ya sanya ta je ta nemawa kanta mafita don kar ta rako sauran mata.

A duk lokacin da tsamarsu ta tashi, shi kuma Stephen na zagin matar tasa da cewa ita karya ce wacce namiji guda daya baya gamsar da ita.

Sai dai a ranar Asabar din da ta gabata ne, Stephen ya nemi ya yi tufkar hanci ta hanyar yin amfani da damar fita da matarsa ta yi zuwa shagon sayar da maganinta, inda a nan ne ya kira yaran nasa guda 4 ya yi musu kallo na tsanaki, inda daga bisani ne ya dauki wata sharbebiyar wuka ya yi ta daba musu har sai da suka ce ga garin ku nan. Kuma da ya ke kanwar matar tasa tana gidan, ita ma ya hada da ita ya yanka.

Bayan ya kamma aika-aikan nasa ne sai Stephen ya koma wani lungu a gidan nasu ya boye kansa ya kuma bude kwalba guda na guba ya kwankwade, dalilin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa shi ma.

DPO na ‘yan sandan yankin Awada, Mista Martin Mbajunwa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da bincike, a yayin da gawarwakin ke ajiye a wajen ajiye gawa na yankin.