
Rundunar ƴan sanda a jihar Kwara da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta cafke Issa Naigheti da laifin yin garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho tare da karbar kudin fansa har naira miliyan 2.5.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ajayi Okasanmi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Ilorin.
Okasanmi, mai muƙamin Sufeto na ƴan sanda, ya ce jami’an ƴan sanda sun kama Naigheti a ranar 4 ga watan Janairu a kewayen unguwar Kambi, Ilorin, a yayin da ake bin sahun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
“Ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi cewa ya hada baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo, kuma ya karbi Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa.
“Ana ci gaba da kokarin kama sauran wadanda suka aikata laifin, kuma za a mika su zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin,” in ji Mista Okasanmi.