Home Ƙasashen waje Wani mutum ya kashe mutane 10 da bindiga a babban kanti a Amurka

Wani mutum ya kashe mutane 10 da bindiga a babban kanti a Amurka

0
Wani mutum ya kashe mutane 10 da bindiga a babban kanti a Amurka

Ƴan sanda sun ce wani ɗan bindiga ya kashe mutane 10 a wani kantin sayar da kaya na Walmart da ke Chesapeake a jihar Virginia ta Amurka.

Rahotanni sun ce mutumin, wanda manajan kantin ne, ya bude wuta sannan ya juya bindigar ya harbe kansa nan take.

Shugaban ƴan sanda na birnin Chesapeake ya wallafa a shafinsa na twitter “‘yan sanda sun tabbatar da wani harin da ya faru tare da asarar rayuka a Walmart”.

Akwai ‘yan cikakkun bayanai, amma wani dan sanda ya yi magana game da “mutane 10” da aka kashe tare da raunata da yawa.

Har yanzu babu wani dalili na harin da ya fito a birnin da ke gabar tekun gabashin Amurka.