Home Labarai Wani mutum mai shekara 55 ya mutu a kogi a Hadeja

Wani mutum mai shekara 55 ya mutu a kogi a Hadeja

0
Wani mutum mai shekara 55 ya mutu a kogi a Hadeja

Wani mutum mai shekara 55, mai suna Sulaiman Potiskum ya mutu bayan ya nutse a wani kogi da ke karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa.

Badarudeen Tijjani, kakakin hukumar tsaron farar hula, NSCDC, reshen jihar Jigawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Dutse.

Tijjani ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:45 na safe, lokacin da marigayin ya je yin wanka a kogin.

“Wani Sulaiman Potiskum mai shekaru 55 ya rasa ransa a wani kogi da ke Gada a yankin Bakin Kogi a Hadejia.

“Mummunan lamarin ya faru ne a lokacin da marigayin ya yi yunkurin yin wanka a bakin gabar kogin, amma igiyar ruwa ta tafi da shi,” in ji shi.

Tijjani ya ce, tawagar jami’an neman gawarwaki da masunta ne su ka dauko gawar Suleman din, inda ya ce daga baya ma’aikatan lafiya a babban asibitin Hadejia suka tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce tuni aka mika gawar marigayin ga iyalansa domin yi masa jana’iza.