
Hassan Y.A. Malik
Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da fulani suka kaddamar akan wani kauye mai suna Olosu, cikin karamar hukumar Okpokwu da ke jihar Binuwai.
Shugaban karamar hukumar ta Okpokwu, Mista Ogwuche Olofu, ya tabbatar da faruwar harin ga gidan talabijin na Channels TV.
Mista Olofu ya bayyana cewa, fulani makiyaya sun kaddamar da hari akan ‘yan kauyen Olosu jiya Litinin 5 ga watan Maris, 2018 a matsayin ramuwar gayya da suka ce sun yi na harin da matasan kauyen Olosu suka fara kai musu wanda babu wanda ya san lokacin da hari na farkon ya faru.
Ya ci gaba da cewa, harin na fulani makiyaya ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 17, inda har yanzu akwai wasu da ba a gani ba, la’alla ko sun mutu ko kuma an yi garkuwa da su.
Sai dai har zuwa lokacin da muka kallama hada wannan rahoto, ‘yan sada a jihar ta Binuwai ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba.
Wannan hari da ya faru ne awanni kadan bayan da fadar shugaban kasa ta sanar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihohin da ke fama da tashe-tashen hankula da suka hada da Zamfara, Ribas da jihar ta Binuwai.
A ranar 11 ga watan Janairu ne dai gwamnatin jihar Binuwai ta gabatar da jana’izar mutane 71 da harin fulani makiyaya ya salwantar da rayuwarsu. Kuma tun bayan wannan lokaci ne dai aka ci gaba da samun irin wancan hare-hare a can da can, inda rayuka da dukiyoyi ke ci gaba da salwanta.