Home Nishaɗi ‘Warr’: Ba zan ƙara cewa komai ba — Ado Gwanja

‘Warr’: Ba zan ƙara cewa komai ba — Ado Gwanja

0
‘Warr’: Ba zan ƙara cewa komai ba — Ado Gwanja

 

Fitaccen mawaƙin Hausa na zamani, Ado Isa Gwanja ya ce a halin yanzu babu abin da za a ji daga bakinsa a kan abubuwan da su ke faruwa da shi game da waƙoƙin sa.

Gwanja ya yi wannan taƙaitaccen bayanin ne a lokacin da mujallar Fim ta tuntuɓe shi a kan haramta waƙar sa ta ‘Warr’ a gidajen rediyo da talbijin da Hukumar Kula Da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC) ta yi.

Haka-zalika, wasu lauyoyi 9 sun shigar da ƙorafi a kotun Shari’ar Muslunci a kan waƙar ‘Chas’ da Gwanja ɗin ya yi, lamarin da ya haifar da cecekuce tsakanin masu amfani da kafafen sadarwa na zamani.

Gwanja ya faɗa wa mujallar cewa, “Yanzu kam ba abin da za a ji daga baki na. Kawai na yi shiru kawai. Ba zan kuma magana ba, saboda ina so in jira in ji.”