Home Siyasa Wasu ƴan APC sun nemi kotun taraiya da ta hana babban taron jam’iyar na ƙasa

Wasu ƴan APC sun nemi kotun taraiya da ta hana babban taron jam’iyar na ƙasa

0
Wasu ƴan APC sun nemi kotun taraiya da ta hana babban taron jam’iyar na ƙasa

 

Wasu fusatattun ƴan jam’iya mai mulki, APC sun garzaya zuwa Babbar Kotun Taraiya a Abuja domin ta hana shugabancin riƙo na Mai Mala Buni shirya babban taron jam’iya na ƙasa a watan Febrairu.

Waɗanda su ka shigar da ƙarar a ranar 4 ga watan Janairu, sun haɗa da Suleiman Dimas Usman, Muhammed Shehu, Samaila Isahaka, Idris Isah, da kuma Audu Emmanuel.

Lauyan masu ƙara, Olusola Ojo, shine ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022.

Masu ƙarar sun ce yin babban a Febrairu taron zai saɓawa kundin tsarin dokokin APC.

Sun ƙara da cewa rashin yin zaɓukan shugabannin jam’iya na jiha a dukkanin jihohi 36 na ƙasa gami da Abuja, APC ba ta da ikon shirya taron.

Sun ƙara da cewa APC ta yi zaɓukan shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34, amma ba ta yi a Jihohin Anambra da Zamfara ba.

Waɗanda a ke ƙara sun haɗa da Jam’iyar APC, Shugaban Kwamitin Riƙo na APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.

Kawo yanzu dai, kotun ba ta sanya ranar da za ta saurari ƙarar ba.