
Wani bidiyo da ya karaɗe gari a Indiya ya na nuna wasu ma’aurata na barar kuɗi domin karɓo gawar ɗan su a asibiti ya tada kura a kasar.
BBC Hausa ta rawaito cewa ma’auratan sun shiga wannan yanayi ne bayan ma’aikatan asibiti sun bukaci su biya kuɗi mai yawa kafin a ba su gawar ɗansu.
Asibitin ya ce zai bincike lamarin domin daukar mataki.
Halin da iyayen yaron suka fada na sake nuna mawuyancin hali na galabaita da dubban iyalai ke ciki a Indiya, da cin hanci a fanin lafiya.
Mahesh Thakur da matarsa, sun shaida wa kafar yaɗa labarai na ANI, cewa da fari ɗan nasu ya bata na tsawon kwanaki.
Daga baya kuma, aka kira su a waya da sanar da su cewa ya mutu – kuma ba su san abin da ya yi ajalinsa ba, kawai an ce an ga gawarsa a wani asibiti.
Sannan da aka je asibiti, sai ma’aikata suka buƙaci su biya kuɗi har rupee dubu 50, kwatankwacin dala 643 kafin a basu gawar.
Ma’auratan cikin yanayi na tausaya ga talauci ya kasance ba su da zabi sama da shiga gari su yi bara domin biyan asibitin.
Wannan yanayi da aka naɗa aka daura a shafukan sada zumunta ya ja hankali da alla-wadai tsakanin ‘yan kasar.
Mahukunta asibitin dai sun ce za su dau hukunci mai tsanani bayan kammala bincikensu.