
Wasu murguza-murguzan tautau kimanin guda miliyan 150 sun yi fitar ɗango za su addabi gidaje a Birtaniya saboda tsananin zafin da aka yi a bana.
Wannan tautau mai kimanin tsawon 7.5cm, ruwan kasa-kasa ne kuma ya saba shiga gidaje a ƙarshen watan Satumba zuwa tsakiyar watan Nuwambar ko wacce shekara.
Zafin da aka yi bana ya sa kwari sun hayayyafa, kuma damunar bana a kasar ta sa ƙwari sun maƙalƙale a jikin yanar ta gizo-gizo.
Wani masanin fannin namun dawa Simon Garrett ya ce shi tautau bai damu da shiga gidan mutane ba domin ya fi samun abinci a waje.
Ya ce ba kasafai wannan kwaro ke watayawa a gidajen mutane ba saboda yawanci ba datti kuma a bushe gidajen su ke kamas.
A cewarsa jima’i ne ya ke sa gizo-gizo ya biyo matarsa cikin gidan mutane.