Home Ƙasashen waje Wata cuta da ba a fayyace ba ta kashe yara 20 a Afghanistan

Wata cuta da ba a fayyace ba ta kashe yara 20 a Afghanistan

0
Wata cuta da ba a fayyace ba ta kashe yara 20 a Afghanistan

 

 

 

Barkewar wata cuta da ba a kai ga fayyace ta ba ta yi sanadin mutuwar yara 20 a kudancin lardin Helmand na kasar Afganistan, in ji daraktan yada labarai da al’adu na lardin Hafiz Rashid a yau Laraba.

Yaran da suka kamu da cutar sun mutu a cikin kwanaki biyu da suka gabata a gundumar Baghran, in ji jami’in.

“Dalilin bullar cutar na iya zama shan gurbataccen ruwa.

Jami’in ya ce wasu da abin ya shafa da suka haɗa da ƙananan yara suna karɓar magani a wata cibiyar lafiya ta yankin.

Rashin samar da ababen more rayuwa da suka hada da cibiyoyin lafiya da kuma samun ruwan sha a yankuna masu nisa na Afganistan ya sa mazauna ƙauyukan ke fuskantar mutuwa sakamakon cututtuka da za a iya warkewa.