Home Labarai Wata jami’ah a kasar Benin ta yi barazanar kai DAILY NIGERIAN kotu

Wata jami’ah a kasar Benin ta yi barazanar kai DAILY NIGERIAN kotu

0
Wata jami’ah a kasar Benin ta yi barazanar kai DAILY NIGERIAN kotu

Biyo bayan binciken da DAILY NIGERIAN ta gudanar kan korafin da dalibai a Najeriya suka yi na yadda wasu ‘yan uwansu dalibai kan garzaya kasar Benin domin samu digirin bogi a cikin shekara guda, musamman wata jami’ah da ake kira ESEP LE BERGER dake birnin Kwatano, jami’ar ta yi barazanar kai wannan jarida kara.

A wata wasika da jami’ar ta aikowa da DAILY NIGERIAN da aka rubuta ranar 12 ga watan Afrilu, 2018. Jami’ar ta yi barazanardaukan mataki na Shariah akan DAILY NIGERIAN matukar wannan jarida bata cire sunan jami’ar a matsayin daya daga cikin jami’o’in da suke bayarda digirin bogi ba.

Idan za’a iya tunawa, bayan da wasu dalibai ‘yan Najeriya suka yi korafi kan digirorin bogi da takwarorinsu suke samowa a kasar Benin a cikin shekara guda. Wakilin DAILY NIGERIAN yaje har kasar domin gudanarda binciken halin da jami’o’in kasar suke ciki.

A saboda wannan ne ma, ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta bayar da sanarwa kin amincewa da duk wani karatun Digiri a kasar Benin da Togo da Ghana da kuma Kamaru.

A cewar ministan Ilimi Malam Adamu Adamu, wannan hukuncin da ma’aikatar ta dauka ya shafi kin daukar ma’aikata masu shaidar kammala karatu a wannan kasa dama fannonin da ba na Gwamnati  ba indai a Najeriya suke.

Acewar sanarwar da ta iso DAILY NIGERIAN cewar matakin da Gwamnati a Najeriya ta dauka, tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da wannan batu.

Masu aiko mana da bayanai sun tabbatar mana da cewar, tuni wasu jami’o’i a kasar ta Benin suka fara daukan matakan yin garambawul ga yadda suke gudanarwa, domin gyara irin kura kuran da suka yi.

Sai dai kuma, Babban Editan jaridar DAILY NIGERIAN Malam Jaafar Jaafar yayi watsi da wannan barazana, ya tabbatar da cewar Jaridar DAILY NIGERIAN na nan kan bakanta kan wancan rahoto da ta fitar bayan bincike da ta yi.

A cewarsa, daya daga cikin makasudin gyara irin wannan a aikin jarida shi ne a bayyana rashawa da illolinta domin aja hankalin hukumomi don daukar matakan da suka dace domin yin gyara.

“A lokacin da muka buga wancan labari da muka bayar, ya ja hankalin da yawan ‘yan Najeriya, inda suka dinga bayyana mana irin yadda halin tabarbarewar ilimi yake a kasar da kuma yadda ake tafka kazamar cuwa cuwar samun digiri, muna da sunaye da yawa, kai har ma da wasu takardun shaidar kammalawa daga irin wadannan jami’o’i”

“Abinda zamu ce dangane da wannan barazana shi ne, DAILY NIGERIAN na nan kan bakanta game da kabarin da ta bayar” A cewar Malam Jaafar babban editan jaridar DAILY NIGERIAN.