
Wata kotun shiyya dake unguwar Ƙarmo a babban birnin tarayya Habuja, ta sa an lakaɗawa wasu mutum uku bulala sakamakon kama su da laifin rara-gefe cikin duhu a lambun wani otal.
Kotun dai ta sa an yiwa Daniel Lucky da Aliyu Ahmed da kuma Badiru Lawal bulala shida-shida kowannensu, sakamakon kama su da akai a daura da lambun otal din Hill Top dake babban birnin tarayyar.
Mutanan dai an kama su ne sakamakon hanayiyarsu da aka ji a cikin lambun otal din.
Alkalin kotun Mai Shariah Abubakar Sadiq ya gargaɗi mutanen da su guji maimaita irin wannan laifi.
Mai shari’ar ya ƙaddamar da hukuncin kan mutanen uku ne bayan da suka amince da laifin da ake zargin su da shi, kuma suka nemi afuwar kotun.
Me gabatar da ƙara, Madam Florence Avhioboh ce ta bayyanawa kotun cewar, ‘yan sintiri a yankin unguwar Utako ne suka kama mutanen.
Ta ce Jimoh Gbende shi ne ya jagoranci sintirin da ya kai ga damƙe mutanen a salasainin daren ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata.
‘Yan sanda dai basu kai ga gano ko mutanen sun yi shirin aikata wani laifi ba, a cewar bayanai.
Me zaku ce kan wannan hukunci, shin abinda aka yiwa mutanen uku ya dace?