
Wata tashar samar da iskar Gaz dake Legas ta kama da wuta ganga-ganga, har ma ta watsu zuwa wasu gurare dake makwabtaka da wajen.
Wannan mummunar gobara ta faru ne da sanyin safiyar Litinin din nan, bayan da aka ji wata fashewa mai karfin gaske a sashin tashar na biyu.
Jami’in hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta FRSC, Bisi Kazeem ya bukaci masu motoci da su kaucewa bin hanyar da gobarar ta auku. Har ya zuwa yanzu ba’a san dalilin wannan gobara ba.
Tuni dai jami’an kashe gobara suka isa wajen.