Home Siyasa WATA SABUWA: Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da tsarin sulhu da uwar jam’iyar APC ta fitar

WATA SABUWA: Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da tsarin sulhu da uwar jam’iyar APC ta fitar

0
WATA SABUWA: Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da tsarin sulhu da uwar jam’iyar APC ta fitar

 

Ɓangaren Jam’iyar APC a Jihar Kano, wanda Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya ƙi amincewa da tsarin da Umar jam’iyar ta ƙasa ta fitar, wanda zai sanya su ma a basu kason su na muƙaman jam’iya a jihar.

A wata wasiƙa mai shafi huɗu, wacce a ka fitar da ita a jiya Litinin, sannan a ka aikewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Shekarau, wanda ya ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, shelkwatar APC ɗin ta naɗa Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da kuma Sanata Abba Ali domin su sa ido a kan yadda za a daidaita al’amura a jam’iyar da kuma sulhunta wa a jihar.

Kamar yadda tsarin rabon muƙamin ya nuna, za a samar da wani gungu na ƙusoshin jam’iya tun da ga mazaɓa zuwa jiha a kowacce Ƙaramar Hukumar da ga cikin Ƙananan Hukumomi 44 sun da a ke da su a jihar.

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa rabon ya fi taimakawa ɓangaren Ganduje sabo da ƴan majalisar wakilai ta taraiya, Sanatoci, ƴan majalisar jiha, kwamishinoni, masu baiwa Gwamna shawara, shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakan su duk su na cikin gungun ƙusoshin jam’iyya da za a samar su daidaita jam’iyar.

Sai dai kuma a wata wasiƙa da su ka sanyawa hannu kuma su ka aikewa Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyar na ƙasa, ƴan ɓangaren Shekarau sun ƙi amincewa da sabon tsarin.

Waɗanda su ka sanya hannu a wasiƙar sun hada da Sanata Ibrahim Shekarau (APC-Kano Central), Sanata Barau Jibrin (APC-Kano North), Tijjani Jobe (APC- mazaɓar D/Tofa/Rimingado ), Nasiru Gabasawa (APC- mazaɓar Gezawa/Gabasawa ), Haruna Dederi (APC- mazaɓar Karaye/Rogo ), Sha’aban Sharada (APC- mazaɓar Kano Municipal ) da kuma Shehu Dalhatu (Shugaban Buhari Support Group).

A cewar su, tsarin da uwar jam’iyar ta ɓullo da shi bai ƙunshi tsarin da a ka ce su bayar na rabon muƙamai ba.

Ɓangaren na Shekarau ya kuma nuna rashin jin daɗin sa kan yadda wasikar da uwar jam’iyar ta turowa ɓangarori biyun a Kano ta isa gurin tsagin Ganduje har a ka fara yawo da ita a kafafen sadarwa, yayin da shi ɓangaren nasu ba su ma ga wasiƙar ba.

Sun nuna cewa ɓangaren na Ganduje ya ta yaɗa wasiƙar da nufin cewa yanzu jam’iyar ta koma ƙarƙashin ikon sa.

“A wannan hali da a ke ciki, mu na masu shaida muku cewa ba mu amince da ɗaukacin abin da wannan wasiƙa ya ƙunsa ba. Bamu yadda ba kuma ba za mu amince ba.

“Mu na kuma masu jaddada goyon bayan mu ga duk wani yunƙuri na ci gaban jam’iyar mu da jagorancin ta,” in ji wasiƙar.