Home Labarai Wata ƙungiya ta bukaci EFCC ta kama Ganduje, a kan bidiyon dala

Wata ƙungiya ta bukaci EFCC ta kama Ganduje, a kan bidiyon dala

0
Wata ƙungiya ta bukaci EFCC ta kama Ganduje, a kan bidiyon dala

Wata kungiya mai zaman kanta, mai suna Yaƙi da Rashin Adalci ta bukaci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC da ta kama tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da gurfanar da shi gaban kotu bisa faifan bidiyo da ke nuna shi yana karbar cin hanci daga hannun ƴan kwangila.

A watan Oktoban 2018 ne jaridar DAILY NIGERIAN ta wallafa faifan bidiyo da ita kaɗai ta sake shi, da ke nuna tsohon gwamnan Kanon na cusa makudan ɗaurin daloli a aljihu babbar riga, wadanda ake kyautata zaton cewa ‘yan kwangila ne su ka kawo masa.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga Mayu, kuma aka aika wa kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano, kuma aka yi kwafin ta zuwa ga ICPC, babban daraktan kungiyar, Ibrahim Umar, ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su sake bude binciken tun da gwamnan ba shi da rigar kariya a yanzu.

“Don haka mun rubuta muku ne domin mu ja hankalin ku kan tsare tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan zargin karbar cin hanci da kuma daukar matakin da ya dace kamar yadda hukumar ku ke yi wa mutane gama-gari.

“Za ku iya tunawa a wani lokaci a shekarar 2018 an yi zargin faifan bidiyo da Malam Jaafar Jaafar, babban editan jaridar Daily Nigerian [wata jaridar yanar gizo] ya wallafa kan cewa tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi cin hanci daga ‘yan kwangila har dala miliyan biyar”.

Kungiyar ta tuno da yadda majalisar dokokin jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan wannan zargi, amma aka dakatar da bayan hukuncin da wata babbar kotun jihar Kano ta yanke.

Yayin da ya ke bayar da hujjar dalilin shigar da korafin, Umar ya lura cewa kungiyar da sauran ‘yan Najeriya na da sha’awar sakamakon binciken.

Ya ce sakamakon binciken zai zama izina ga al’umma kan illar cin hanci da rashawa.