Home Labarai #WeAreEqual: Tinubu ya goyi bayan gangamin samar da daidaiton jinsi a Afirka

#WeAreEqual: Tinubu ya goyi bayan gangamin samar da daidaiton jinsi a Afirka

0
#WeAreEqual: Tinubu ya goyi bayan gangamin samar da daidaiton jinsi a Afirka

A jiya Litinin ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da gangamin #WeAreEqual, wanda aka ƙirƙiro domin rajin daidaiton jinsi da kuma yanke bambancin da ke tsakanin jinsi a Afirka.

Tinubu ya amince da gangamin na #WeAreEqual ne a jawabinsa a wajen kaddamar da shi da kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika, OAFLAD, wadda uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta shirya.

Tinubu ya ce bincike ya nuna cewa ilimi shine ginshikin ci gaban al’umma.

Ya kara da cewa idan aka baiwa ƴaƴa mata damar cimma burinsu, al’umma za su ci gaba, tattalin arziki ya bunkasa, kuma kasashe su yi nasara.

“Gangamin zai tabbatar da gaskiyar cewa ƙarfafa mata da yara mata na da mahimmanci wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya, SDGs.

“Ina jinjina da jajircewa da sadaukarwar matan shugabannin Afirka, OAFLAD, na ciyar da daidaiton jinsi da takaita gibin da ake samu a damammaki da mukamai a fadin nahiyar Afirka.

“Wannan Gangamin, wanda manyan ku suka jagoranta, yana da matukar muhimmanci a gare mu a Afirka. Don haka ina taya ku murna baki daya. Ina taya masoyiyata uwargidan shugaban kasar Najeriya murna ta musamman wacce ta zabi ilimi a matsayin wani babban kudiri na wannan gangami a fadin ƙasar nan.

Shugaban ya kuma shawarci daukacin ‘yan Najeriya da su yada wannan gangami, yana mai cewa ya yi alkawarin baiwa ƴa mace da ke da ilimi damar kawo sauye-sauyen da ya kamata a tsakanin al’ummomin Afirka domin samun ci gaba.