
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya baiwa Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN lambar yabo ta gwarzon ma’aikata na jihar Rivers.
Gwamnan ya bayar da kyautar ne ga Malami a wani taron da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal a ranar Asabar.
Umar Gwandu, kakakin ministan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an baiwa Malami lambar yabon ne sabo da irin gudunmawar da ya bayar wajen kafa makarantar Dokta Nabo Graham-Douglass ta Jihar Rivers na Makarantar Koyon Shari’a ta Najeriya, da dai sauran gudunmawar da ya bayar wajen gina kasa.