
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce bai kai ƙarar ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kotu ba.
Ya bayyana hakan ne yau Juma’a a wani wajen taro da manyan jam’iyyar a birnin Port Harcourt.
BBC Hausa ta rawaito wike ya kara da cewa bai baiwa kowa izinin kai ƙararsu kotu ba.
Tun da fari, wasu jaridun kasar nan sun rawaito cewa Wike da wani ƙusa a PDP mai suna Newgent Ekamon sun shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, inda su ke ƙalubalantar janyewar da Tambuwal yi yi wa Atiku a zaɓen fidda+gwani da kuma goyon bayan Atiku.