Home Labarai Wulakanta Al-Kur’ani kafirci ne – Dr. Bashir Aliyu Umar

Wulakanta Al-Kur’ani kafirci ne – Dr. Bashir Aliyu Umar

0
Wulakanta Al-Kur’ani kafirci ne – Dr. Bashir Aliyu Umar

An gargadi al’ummar Musulmi da su guji wulakanta Al-Kur’ani ta hanyar ajiye shi a kasa, yadda zai bayu zuwa ga wasu su taka shi ba tare da sun sani ba, musamman a wannan lokacin da al’umma da dama suke yin Ibadar I’itikafi a masallatai.

Babban Limamin masallacin Alfurkan dake Kano, Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar ne yayi wannan kiran a lokacin da yake gudanar da Tafsirin al-kurani mai girma na watan Ramadan kamar yadda aka saba a Masallacin Al-Furqan dake Kano.

Malamin ya jawo hankalin mutane ne saboda yawan korafi da ake samu yadda wasu ke yin sakaci suna ajiye Al-Kurani a kasa, wanda hakan yake sanya wasu su taka shi ba tare da sun sani ba,idan bukatar fita daga masallaci ta gaggawa ta kama su.

Haka kuma, Malamin yayi bayin irin yadda masu tozarta Al-Kurani zasu samu zunubbai masu yawa da zai kai mutum zuwa ga aikata Kafirci. Malamin yace duk mutumin da ya wulakanta Al-Kurani ya kafirta.

“Idan mutum ya taka Al-Kurani ba da gangan ba, to zunubin hakan yana komawa ne zuwa ga wanda ya ajiye Al-Kurani a inda za’a taka shi” A cewar Dakta Bashir Aliyu Umar.