
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta cafke wani magidanci mai shekara 33 mai suna Musa Kamson da ke zaune a kauyen Mai-Tunku da ke Dadiya a yankin Bambam ta karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe da kashe tsohon mijin matarsa mai suna Samny ta hanyar sassara shi da adda bisa zargin wai yana bibiyar da matar tasa.
A lokacin da Musa Kamson ke shaidawa manema labarai yadda lamarin ya faru a shedikwatar ’yan sandan jihar Gombe, ya ce ya kama marigayin ne a kan matarsa mai suna Binta Musa lokacin da ta je gonar gyada ita da ’ya’yansa.
Ya ce idan matarsa ta je daji da ’ya’yansa suna komawa gida da karfe goma na safe, a ranar da lamarin zai faru sai ’ya’yan kadai suka koma gida ba mahaifiyarsu. Da ya tambayesu ina mahaifiyar tasu, sai suka ce tana can daji.
A cewarsa tunda safe shi kwarton ya tare ta ya ce su hadu da karfe 11 a gindin wani dutse, kuma wannan alkawarin ne ya sa ba ta koma gida ba tana jiran lokacin alkawarinsu da kwartonta.
Ya kara da cewa yana zaune a gida yana lura ya ga ta inda zai hango dawowarta sai ya hango kwarton ya wuce, can ita ma sai ga ta tana binsa a baya kusa- da-kusa tana haurawa gindin dutsen.
A ta bakin Kamson, “Shi ne sai na dauki adda na bi su, ina isa inda suke sai na tarar suna lalata da juna, shi ne kawai na kashe kwarton,” inji shi.
Ya ce da ya kashe kwarton sai ya kai kansa ga ’yan sanda ya gaya musu cewa ya kashe kwarton da ya kama yana lalata da matarsa a daji.
Ita ma Binta Musa mai shekara 25, kuma tsohuwar matar marigayi Samny da mijinta Musa Kamson ya kashe, wacce ’yar kauyen Mai Tunku ce ta tabbatar da cewa babu shakka mijinta ya kama ta a daji suna hira a gona, shi ne ganinsu tare ya sari tsohon mijin nata wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Ta ce da mijinta ya kashe wanda suke tare sai ta tafi gida ta je ta fadi abin da ya faru shi ne aka sako ta a gaba ta je ta nuna gawar wanda aka kashe din.
Binta Musa, ta ce ta taba auren Samny amma sun rabu bai wuce wata daya ba, sai dai har suka rabu ba su haihu da shi ba.
Yanzu dai Musa Kamson da matarsa Binta Musa suna hannun ’yan sanda ana gudanar bincike kafin a tura su kotu don yanke musu hukunci.