
Daga Mustapha Usman
Tijjani Ado Ahmad, sanannen ɗan jarida da ke Freedom Radio, ya rasu a daren jiya a birnin Atlanta da ke ƙasar Amurka.
Tijjani ya rasu yana da shekara 39.
Wannan ɗan jarida wanda shi ke gabatar da wani shiri da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ke ɗaukar nauyi wato “Greetings from America”, ya je ƙasar ne sati daya da ya gabata don tattaunawa da daliban Najeriya da ke karatu a ƙasar.
A cewar ɗan uwan marigayin mai suna Muhammad, Tijjani ya yi ƙorafin cewa ciwon kai na damunsa, daga bisani sai ya faɗi.
Muhammad ya ce daga nan ne aka ɗauke shi zuwa asibiti don farfaɗo da shi.
“Muna ta magana da likitan tunda aka kai shi asibitin, daga bisani kuma liktan ya kirawo ni ya ce min Tijjani ya rasu” inji Muhammad.
Ana tunanin ofishin jakadancin zai ɗauki ɗawainiyar dawo da gawar Kano don yi masa jana’iza.
Marigayi Tijjani ya rasu ya bar mace daya da ‘yaya biyu.