Home Labarai Yadda aka yi juyin mulkin da ya kai ga kashe Murtala Mohammed akan idonmu – Inji Jibril Aminu

Yadda aka yi juyin mulkin da ya kai ga kashe Murtala Mohammed akan idonmu – Inji Jibril Aminu

0
Yadda aka yi juyin mulkin da ya kai ga kashe Murtala Mohammed akan idonmu – Inji Jibril Aminu
Tsakure daga wata kasida da Farfesa Jibrilu Aminu ya gabatar lokacin muhadarar tunawa da marigayi Murtala Mohammed shekaru 30 da komawarsa ga Allah, sha-uku ga Fabrairun 2006.
Ina jin abin kamar jiya ya faru. A daren washegarin da za a kashe shi, ina gidansa a Legas. Mun sallaci magriba da isha tare, daga nan muka ci abincin dare, ba wani abinci name na musamman muka ci ba. Muna zaune, sai ga wasu latirishan (masu gyaran lantarki) sun shigo, suka ce sun zo gyara wutar da tayi coci. A zahiri kuma a lokacin babu wani coci ko tartsatsi da ya faru. Sai Janar Murtala yace min, “rabu da su, soja ne”. Tun da suka shigo ban aminta da su ba, sai daga baya na gane makircin zuwan. Nan dai muka gama hira na tashi na barshi, ashe ban sani ba, gani na da shi na karshe kenan.
A washe garin ranar, na tuko mota daga masaukina a Alagbon Close, ikoyi zuwa wajen aiki, mun samu jinkiri na babu gaira bare dalili. Ashe bamu sani ba, wani mugun alkaba’i na faruwa bisa hanya, don mun hangi wani dan koriya, ya kafe motarsa a tsakiyar titi ya shek’a a guje.
A lokacin da muke karasowa, guri duk ya hautsine. Nan muka hangi wata motar soji mak’are da mutane, wasu kuma na biye da su a guje a kas. Suka bazama sai Tashar watsa labaru ta Legas. A lokacin ta bayyana cewar, wani mummunan bala’i ya faru. Ashe dai sojoji ne suka yi juyin mulki. Bayan da aka muka ji an ana ruwan harsasai da harbin kan-mai uwa da wabi a kusa da makabartar Ikoyi.
Bayan kamar mintuna goma sha biyar, bayan da cikin tsoro da firgici muke fake a ofishin ministan albarkatun gona ne, muka ji sanarwar Kanar Dinka na batun samun mummunar batarnakar da ta faru bayan juyin mulki. Daga baya muka samu labari me firgitarwa na kashe Janar Murtala a cikin motarsa a kusa da mahadar titunan Ikoyi inda daman ta nan na biyo, Allah ne  ya auna min arziki ban iso inda aka yi wannan balahira ba. Galibin abinda ya faru a wannan rana ya auku akan idonmu, dan muna labe a kusa da inda abin ya faru. Allah ya jikan Janar Murtala Mohammed.