Home Kanun Labarai Yadda Alƙalan Dakali a fadar Shugaban ƙasa suka naɗa ɗan ƙasar Chadi a matsayin Shugaban hukumar leƙen asiri ta Najeriya

Yadda Alƙalan Dakali a fadar Shugaban ƙasa suka naɗa ɗan ƙasar Chadi a matsayin Shugaban hukumar leƙen asiri ta Najeriya

0
Yadda Alƙalan Dakali a fadar Shugaban ƙasa suka naɗa  ɗan ƙasar Chadi a matsayin Shugaban hukumar leƙen asiri ta Najeriya
Sabon Shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Rufai Abubakar

Abun tambaya ne kwarai da gaske, ace me yasa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yardaya amince da naɗin Ahmed Rufai Abubakar amatsayin Darakta Janar na hukumar leƙen asiri ta Najeriya, NIA, duk kuwa da cewar rashin kwarewarsa kan wannan aiki a bayyane take, uwa uba kuma, yana da takardun kasancewa dan ƙasar Chadi.

A ranar 12 ga watan Afrilun 2017, hukumar dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC, ta gano wasu maƙudan kudaden kasashen waje da na Najeriya da suka kai zambar kudi dalar amurka miliyan $43.4, da kuma fan na ingila £27,800, da kuma Naira miliyan 23.2 a wani ginin bene mai hawa bakwai, akan titin Osbrne, dake Ikoyi a Legas.

Darakta Janar na hukumar NIA na lokacin Ayo Oke, shi ne ya mallaki wadannan maƙudan kudade, inda yace, maƙudan kudaden na hukumar tasa ne.

Mako guda bayan da hukumar EFCC ta bayyana gano wadannan boyayyun kudade, Shugaban kasa ya bayar da sanarwar dakatar da Ayo Oke daga mukaminsa, sannan ya umarci a gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan yadda aka yi hukumar NIA ta mallaki wadannan zambar kudade, sannan da batun yadda aka yi aka jibge wadannan tarin kudaden haka, sannan a bincika shin ko akwai sabawa doka da kuma batun sha’anin tsaro a yadda aka aje wadannan maƙudan kudade.

Biyo bayan wannan umarni na Shugaban ƙasa na bincikar babban jami’i a hukumar NIA, a sabida haka aka baiwa jakadan Najeriya dake kasar Chadi Mohammed Dauda umarni ya riƙe mukamin Darakta Janar na riko kafin kammala binciken babban darakta hukumar.

Kwamitin binciken wanda aka kafa shi karkashin jagorancin mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo tare da Attoni janar na kasa kuma Ministan Shari’ah Abubakar Malami SAN, da kuma mai baiwa Shugabankasa shawara na musamman akan abinda ya shafi tsaron kasa Babagana Monguno a matsayin mambobin kwamitin su biyu, yayinda mataimakin Shugaban kasa ya jagoranci kwamitin.

Bayan kammala aikin wannan kwamiti karkashin mataimakin Shugaban kasa yemi Osibanjo, kwamitin ya mika rahotonsa, daga bisa ni kuma, shugaban kasa ya sake kafa wani kwamiti da zai duba wannan rahoto da Mataimakin Shugaban kasa ya gabatar karkashin jagorancin Babagana Kingibe tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya. Haka kuma, tsaffin daraktocin hukumar uku, Albert Horsfall, Zakari Ibrahim da kuma Ezekiel Oladeji sun kasance membobin Kwamtin Kingbe, sannan kuma mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan huldodin Diflomasiyya Ahmed Rufai Abubakar ya kasance sakataren kwamitin.

Kimanin wata guda bayan da Babagana Kingibe ya mika rahotonsa ga Shugaban kasa, sai Shugaban kasa ya bayar da sanarwar nadin Ahmed Rufai Abubakar a matsayin Darakta Janar na hukumar da zai gaji wanda aka dakatar. Daga nan kuma cecekuce ya barka akan dacewar sabon daraktan hukumar kasancewar shi ba jami’in tsaro bane, a sabida haka kake ganin rashin cancantarsa wajen rike wannan hukuma.

Ahmed Rufai Abubakar, wanda kafin nadinsa a wannan mukamin, yayi aiki a matsayin mai yiwa Shugaban kasa tafinta a harshen Larabci da kuma Faransanci. Ya ya taba aiki da hukumar ta NIA reshen jihar Katsina lokacin da Zakari Ibrahim ke matsayin Darakta janar a shekarun 90’s amma daga bisani aka sallame shi daga aiki a hukumar sabida ya kasa cin jarabawar karin matsayi har sau biyu.

“Ya kasance a mataki na 12 a ofishin hukumar kula da ma’aikata ta jihar Katsina, lokacin da akai masa canjin wajen aiki a wani yanayi mai cike da rudani, daga nan Darakta Janar na hukumar Zakari Ibrahim ya mayar da shi matsayin mataki na 14 wanda ya sabawa dokar aikin Gwamnati”

“Ya zauna a jarabawar karin matsayi har sau biyu amma bai samu nasara ba. Ahmed Rufai Abubakar daga nan yai ritaya ta kashin-kai a shekarar 2013 domin kaucewa korarsa”

Ya taba zama mataimaki na musamman ga Kingibe a lokacin da yake aikin samar da zaman lafiya a wasu rikice rikice a wasu kasashen Afurka da ke fama da hayaniya, kasancewar yana da kwarewa a harshen Larabci da Faransanci.

DAILY NIGERIAN ta kuma tabbatar daga majiya mai tushe cewar, Shi Darakta Janar din haifaffen kasar Chadi ne, haka kuma,karatunsa na Firamare da Sakandire duk a can kasar yayi su.

Akwai binhu a hukumar dangane da mutumin da aka baiwa jagorancinta kasancewar yana da takardun zaman sa dan kasar Chadi, duba da cewa hukumar leken asiri ta kasa guri ne na musamman.

“Sam samkasar Chadi bata baiwa Najeriya hadin kai ba, a yakin da Najeriyar take yi da kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi. Sabida haka, taya dan asalin kasar Chadi, wanda yake da iyalai da dangi da yawa a can zai jagoranci wannan muhimmiyar ma’aikata?

“Bayan haka kuma,babu adalci a nada manyan mukamai da suka shafi tsaron kasa na gida da na waje duk daga jiha daya wato katsina. Ko dai Gwamnati ta cigaba da rike Mohammed Dauda a matsayin Darakta Janar na hukumar duba da kwarewa da kuma gogewa irin tasa da kuma tarihin ayyukan da yayi cikin nasara ko kuma Gwamnati ta nada wani mutum daga kudancin kasarnan domin daidaita rabon mukamai”

“Amma yin irin wadannan nade naden muhimman mukamai da suka shafi tsaro kuma duk su fito jiha daya da Shugaban kasa, wannan ba adalci bane, yafi kama da kama-karya. Indai aka dore akan haka, Shugaban kasa baya taimakawa da kasarnan ta fannin zaman lafiya da zama dunkulalliyar kasa”

“Wannan mukamin ya kmata ace an tura shi ne zuwa yankinkudu maso gabas, domin daidaita batun sha’anin tsaro a Najeriya” A cewar wani jami’in tsaro da ya tabbatarwa da DAILY NIGERIAN.

Haka kuma, wannan majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewar, fAlkalan dakali dake adar Shugaban kasa, wanda dan uwan Shugaban kasa Mamman Daura yake jagoranta, shi ne yake da hannu dumu dumu wajen nada Ahmed Rufai Abubakar, bisa la’akari da cewar an warewa hukumar dalar Amurka miliyan 44 kari akan kasafin kudin da akai mata.

“Idan ka dauke batun dalar AMurka miliyan 43 da Ayo ya boye a wani gida a Legas, wasu sanannun mutane na son yin watandar wadannan kudade dala miliya $44da aka warewa NIA” A cewar majiyarmu.

Haka kuma, Majaiyar ta kara bayyana mana cewar, Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Abba Kyari da Babagana Kingibe da Zakari Ibrahim na da hannu wajen cusa Ahmed Rufai Abubakar a matsayin Darakta Janar na hukumar NIA din domin samun juya asusun hukumar yadda suka ga dama, duk da daman suna da masaniyar yana da takardun zama dan kasar Chadi da kuma rashin cancantarsa a wannan mukamin.

Mai taimakawa Shugaban kasa kanmu’amala da ‘yan Jarida Garba Shehu, yaki amsa kiran waya kuma yaki maida da martanin sakon tes da aka aika masa kan wannan batun domin jin me fadar Shugaban kasa zata ce kan wannan labari.