
Wani ɗalibi na babban aji a Kwalejin Ilimin Addinin Musulunci ta Elkanemi da ke Maiduguri, a Jihar Borno ya yanka makogoron wani ɗalibi na ƙaramin aji mai suna Jubril Mato, ɗan shekara 11 a makarantar.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Jubril, wanda a halin yanzu ya ke jinya a sashin kula da marasa lafiya mai tsanani na asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, ya fuskanci hukuncin ne saboda ya ƙi zuwa aiken ɗalibin na babban aji.
“Dalibin makarantar a babban aji na SS2, ya aiki Jubril amma bai je ba. Shine ya laɓaɓo cikin dare ya ɗauke shi ya kai shi wani wuri inda ba kowa, sai ya yi amfani da reza ya yanke masa wuya sosai, wanda hakan ya yi sanadin raunata yawancin jijiyoyin wuya da maƙogwaron sa,” inji wata majiya daga makarantar.
Ɗalibin babban ajin, a cewar majiyar, wanda hukumomin makarantar suka ɓoye sunansa, ya bar marigayin cikin jini kace-kace kuma ya zaci ya rasu. Bayan wasu mintuna, sai Jubril ya samu ya yunƙura ya kai kansa ofishin Shugaban makarantar, kafin daga bisani ya faɗi cikin halin rai-kokai mutu-kokai.
An garzaya da Jubril zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri kuma an kwantar da shi a cikin mawuyacin hali a sashin kula da matsananciyar rashin lafiya.
An kama wanda a ke zargi da aikata laifin, wanda aka ce an cusa masa wasu abubuwan da suka gurɓata tunanin mutum, inda daga bisani aka mika shi ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike.
Lamarin, a cewar majiyar, ya faru ne a ranar Asabar 16 ga watan Janairun 2022 amma hukumar makarantar ta boye shi da nufin kada jama’a su sami labari.
An dai ce Jubril, ɗan marigayi Mai shari’a Sadi Mato ne na Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Kano, kuma mahaifiyarsa Hajiya Aisha ta sake auren wani babban ma’aikacin gwamnatin Jihar Yobe.
Sai dai kuma abin takaici ga dangin Jubril, shi sabon mijin mahaifiyar tasa, wanda hukumar makarantar ta kira shi jim kadan bayan faruwar lamarin, ya hana mahaifiyar yaron ta yi rahoton lamarin.
Wani ma’aikacin kwalejin, wanda shi ma ya zanta da ‘yan jarida ya tabbatar da cewa, batun Jubril Mato ba shi ne na farko ba domin an sha samun irin wadannan abubuwa da dama da suka faru a kwalejin amma mahukuntan makarantar sun ci gaba da boye abubuwan, in da hakan ya haifar da ƙaruwar. laifin.
“Wannan ba shi ne karon farko da ake samun tashin hankali da makami a kwalejin ba. Akwai wasu kararraki da dama da suka shafi cin zarafi da cin zarafi da makami, amma hukumar makarantar ta ɓoye maganar. Wannan na iya nufin muna kara haifar da wasu wadanda abin ya shafa sakamakon gazawar da muka yi,” in ji malamin.