
Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi masa tarnaki wajen zama Gwamnan jihar Adamawa a zaben jam’huriya ta uku karkasshin rusasshiyar jam’iyyar SDP.
Boss Mustapha ya bayyana cewar, babu wanda ya kaishi fahimtar rikicin cikin gida na jam’iyya, inda yace “Aatiku Abubakar ya so kakaba min dan takarar mataimakin gwamna, ni kuma naki amincewa da dauki dora, wanda hakan ya zamar min tarnaki wajen zama Gwamnan Adamawa”
“Atiku Abubakar ya hada kai da dan takarar rusasshiyar jam’iyyar NRC, marigayi Saleh Michika, domin a kayar da ni dan naki aminta da kakaba min dan takarar mataimakin Gwamna a wannan zaben”
Sakataren Gwamnatin tarayyar yana wannan jawabi ne wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta kasa reshen jihar Adamawa, a kokarin zaben sabbin Shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai da za’a gudanar nan gaba.