Home Labarai Yadda Ganduje ya kore mu daga APC haka mu ka sallame shi a siyasar Kano

Yadda Ganduje ya kore mu daga APC haka mu ka sallame shi a siyasar Kano

0
Yadda Ganduje ya kore mu daga APC haka mu ka sallame shi a siyasar Kano

Kakakin Kwamitin Kamfe na Jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori wasu kusoshi da dama a jam’iyyar APC a Kano, inda ya ce dukkan su yanzu sun koya wa gwamnan darasi irin na siyasa.

Kofa, wanda ya zama zaɓaɓɓen dan majalisar wakilai ta tarayya, ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV a jiya Laraba.

Ya ce “tun da dadewa ina da alaka mai karfi da jagoran NNPP na ƙasa Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya koya min siyasa.

“A daya bangaren kuma, ba a son zaman mu a APC. Gwamnan baya son da yawar mu a jam’iyyar, shi ya sa ya riƙa yin yadda zai yi ya kore mu da ga jam’iyyar.

“Shi (Ganduje) yana fada da mu, ya tabbatar ba mu samu komai ba, ba mu iya numfashi a APC ba.

“sai mu ka fice mu ka tattara kan mu mu ka fice, sannan mu ka koya masa darasin siyasar da ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa.

“Kuma a karshen wannan rana, ya haifar wa da APC asarar ‘yan majalisar wakilai 18, ciki har da wakilai kusan shida ko bakwai da jiga-jigai ne.

“Ya yi wa APC asarar ƴan majalisar jiha 34 kuma ina mai tabbatar maka da cewa dukkan su masu nagarta ne,” in ji Kofa.