
Ƙungiyar Ohaneze Ndigbo ta ce ɓangaren inyamirai ba za su yadda a basu gurbin mataimakin shugaban ƙasa a takarar zaɓen 2023 ba.
Ta yi wannan iƙirarin ne a yau Alhamis ta bakin Shugaban ta, Farfesa George Obiozor a taron Imeobi Ohaneze Ndigbo a Enugu.
Ya ce yaƙin neman yankin inyamirai su samu shugaban ƙasa wani yaƙi ne da idan a ka yi masa kallo ma tsanaki za a ga cewa ya dace.
A cewar sa, duk wani batu da kace-nace da a ke yi a kan batun shiyya a na yi ne da niyyar a daƙile ɓangaren inyamirai.
“Sabo da haka ina kira ga duk wasu ƴan takarar shugaban ƙasa daga wannan yankin da su dage, su jajirce su kuma saka imani a zuciyar su.
Obiozor ya kuma bayyana cewa Kwamitin Makomar Siyasar ya kin zai gana da duk wasu masu faɗa a ji a ƙasar nan domin shawo kansu su yarda da dalilan da su ka sanya su ke kiraye-kirayen a baiwa inyamirai mulkin ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga duk wani inyamiri da ya bada goyon baya wajen wannnan yaƙin neman zaɓen.