
Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Abubakar Bagudu, a ranar Alhamis da ta gabata, ya rabawa talakawa da manoma kudade kyauta akan hanya.
Wani ganau ya shaidawa DAILY NIGERIAN a ranar Asabar cewar, Gwamnan yayi ta rabon kudade a lokacin da ya fita rangadin ganin gonakin shinkafa a kauyen Matankari a yankin karamar hukumar mulkin Suru a jihar Kebbi.
Haka kuma, Gwamnan ya shiga cikin kasuwa, inda ya dinga rabawa kananan ‘yan kasuwa kudi.