Home Labarai Yadda jami’in VIO ya ci zarafi na — Direban gingimari

Yadda jami’in VIO ya ci zarafi na — Direban gingimari

0
Yadda jami’in VIO ya ci zarafi na — Direban gingimari

 

 

 

Wani direban gingimari mai suna Suleiman Adams, a yau Alhamis ya yi zargin cewa wani jami’in Hukumar Binciken Ababan-hawa, VIO, reshen Kubgbo,, da ke babban birnin tarayya, FCT, ya ci zarafinsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Direban ya fito ne daga Nyanya lokacin da jami’an hukumar VIO suka tare motarsa ​.

Direban ya shaida wa NAN cewa jami’an hukumar ta VIO sun umarce shi da ya bude kofar momotarsa, inda ya ƙara da cewa ya buɗe kofar motar tasa kamar yadda su ka Umar ce shi.

A cewar direban, ya tambayi jami’an VIO ɗin cewa ko ya yi laifi ne da ya shiga Abuja kafin karfe 10:00 na safe.

Adams ya kara da cewa wadannan jami’an na VIO sun taba tare shi kuma suka ce kada ya shiga Abuja kafin karfe 10:00 na safe.

“A lokacin da na tsaya da mota ta, sai wani Haruna Husseni, wani jami’in VIO ya kwaɗa min mari ba gaira ba dalili, ya kuma ja ni zuwa ofishinsu da ke Kugbo.

“Lokacin da muka isa ofishinsu, Husseni ya sake mari na yana duka ma da ƙafa har sai da na fadi kasa,” in ji shi.

NAN ta kuma ruwaito cewa, a wata hira da aka yi da direban babbar motan da yai zargin an ci zarafin sa, kwamandan VIO na Kugbo, wanda ya shaida lamarin, ya aika da jami’an ƴan sanda a Karu domin kama wakilin NAN ɗin.

Sai dai a lokacin da jami’an ƴan sandan suka zo, sai su ka ƙi kama wakilin NAN ɗin, inda suka ce yana gudanar da aikinsa ne da doka ta bashi dama.