Home Labarai Yadda Kwanturolan Kwastam ya fadi ya kuma mutu a filin jirgin sama na Kano

Yadda Kwanturolan Kwastam ya fadi ya kuma mutu a filin jirgin sama na Kano

0
Yadda Kwanturolan Kwastam ya fadi ya kuma mutu a filin jirgin sama na Kano

Kwanturolan da ke kula da sashen kasuwanci na Hukumar Kwastam ta Ƙasa, NCS, Anthony Ayalogu, ya rasu.

A cikin wata sanarwa da sashin hulda da jama’a na hukumar kwastam, AA Maiwada ya fitar, ya ce bayan da Ayalogu ya shiga mawuyacin hali, sai aka garzaya da shi asibitin sojojin saman Najeriya da ke Kano, inda a nan sai likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.

“Ya na kan hanyarsa ne a kan wani aiki na hukuma kwatsam. Daga saukar da a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano sai kawai ya kamu da rashin lafiya, inda kafin kace kwabo ya suma.

“Duk kokarin da aka yi na farfado da shi bai yi nasara ba yayin da aka tabbatar da mutuwarsa a daidai ƙarfe 8:20 na dare a ranar Litinin, 17 ga Oktoba, 2022 a Asibitin Sojan Sama na Najeriya 465 Kano. Yana da shekaru 57, “in ji shi.

A cewar Maiwada, Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali (rtd), yayin da yake jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki Ayalogu, ya ce za a yi kewar marigayin sosai.