
Mafarauta sun samu nasarar cafke wasu da a ke zargin masu garkuwa da mutane ne guda uku a maɓoyar su, kusa da yankin Ossra-Irekpeni a kan hanyar Okene-Lokoja-Abuja.
Ɗaya da ga cikin mafarautan da su ka kai sumamen ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa sai da a kai musayen wuta kafin su damƙe mutanen.
Ya ce mafarautan, tare da shugaban Ƙaramar Hukumar Adavi, Joseph Samuel Omuya, su ka kutsa kai cikin dajin bayan samun bayanan sirri.
Mafaraucin ya baiyana cewa , bayan sun shiga jejin, sai masu garkuwa da mutanen su ka fara buɗe wuta, sai mafarautan su ka maida martani.
“Nan da nan muna muka buɗe musu wuta har mu ka samu nasarar damƙe uku daga ciki,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa wasu daga cikin ƴan ta’addan sun tsere da raunukan bindiga a jikin su.
Bayan Omuya ya yabawa mafarautan a bisa ƙoƙarin da su ka yi na kama ƴan ta’addan, ya kuma yi kira ga mazauna ƙauyuka da su zama su na jajircewa wajen tsaro.