
Wata mace mai shekaru 29 da haihuwa, kuma ‘yar asalin kasar Kanada, Lauren, ta bayyana yadda aka yi ta samu juna biyu ba tare da ta sadu da namiji ba.
News AU ta rawaito cewa, Lauren ta girma ne da wata tawaya a can cikin jikinta da a kimiyance ake kira da hypopituitarism. Wannan na nufin nakasar sashen halittarta da ke aika sako zuwa ga bangarorin jiki da ke sanya jiki ya hauhawa, wanda haka ke haifar da girma da habakar jiki. Shi kuma girma da habakar jiki na da tasiri wajen rika ko balagar sassan jiki da ke da alaka da tarawar mace da namiji.
Hakan ya sanya Lauren ta taso habakar jikinta ba irin na sauran sa’anninta ba. Ta ce, “Wannan dalili ya sanya jinkiri a balagata. A lokacin da sa’anni na suka yi nono ruguza-ruguza, ni kuwa na kasance kwaila, da kirjina a shafe.
A dole na fara amfani da kwayar thyroid da ke sanya jiki ya habaka, tare da karbar allurar habaka sinadaran girma da ke jikina duk kuwa da kasancewar likitoci da abokan arzuka sun ja kunnena akan illar hakan.
Babbar matsalata ita ce ta yadda zan dauki ciki da irin yanayin halitta ta. Koda yake dai wani kwarrarre a fannin ya fada min zan iya daukar ciki, amma sai dai a saka min kwan halittar wata macen a mahaifata a lokacin da zan tara da namiji, amma haka na bukatar kashe dubban daloli don gudanar da wani aiki da ake kira da IVF. Amma duk da haka sai likitan ya tura ni wata cibiya da ake magance rashin haihuwa.
Na dau kimanin shekara guda ina jira layi ya zo kaina a asibitin magance matsalar rashin haihu, amma bayan na samu damar gani kwarrare a wannan fanni na tsawon minti biyar kacal, sai komai ya canja.
A maimakon na bi doguwar hanyar da sai namiji ya tara da ni kafin na dau ciki, sai na zabi hanyar a sanya min kwan halittar namiji a mahaifata. Kuma hakan aka yi, yanzu ina dauke da juna biyu, kuma zan haife abinda na ke dauke da shi a watan Yuni.
A lokuta da dama a yanzu nakan ji kamar na nemi wani wanda zai kawar min da budurcina, amma sai wannan tunani ya kau cikin gaggawa.
Na yi samari da dama daga lokaci zuwa lokaci, amma babu dangantakar da na yi da shakuwarmu ta kai na tara da saurayin nawa na wannan lokacin.