
Daga Hassan Y.A. Malik
Gwarzon dan wasan Barcelona da tawagar kwallon kafa ta Argentina, Lionel Messi, ya bayyana yadda ya ke yi wa kansa allura a duk daren duniya a lokacin yana yaro.
Messi ya bayyanawa America TV a wata ganawa cewa an haifi shi da tawayar sinadarin jiki da ke saka habakar jiki, wanda haka ya sanya a dole sai da aka dinga yi masa allura mai dauke da wancan sinadari na haba jiki a kafafunsa.
“Allura ce ‘yar kankanuwa kuma bata da zafi ko kadan. yau da gobe ya sanya na saba da allurar kuma na iya yi wa kaina. Na ci gaba da yi wa kaina allurar har zuwa lokacin da na cika shekaru 14,” inji Messi
Messi ya ce, iyayena na kashe dalar Amurka $1,500 a kowane wata a wajen yin wannan allurar, har sai da kungiyar da na ke taka wa leda a lokacin, Newell’s Old Boys ta ci gaba da biyan kudaden
Messi ya dawo da iyayensa Barcelona a shekarar 2001, a lokacin yana da shekaru 13, inda kungiyar Barcelona ta ci gaba da biyan wadannan kudade har zuwa lokacin da aka kammala wannan jinya, a lokacin Messi na da shekaru 14 da haihuwa.