
Yusuf Buhari dan Shugaba Muhammadu Buhari ya samu mummunan hadarin babur da yayi sanadiyar jin rauni akansa. Lamarin dai ya auku ne a ranar talatar da ta gabata a yayin da Yusuf Buhari da abokansa suke wasan tsere a unguwar Gwarinfa.
A yayinda Yusuf Buhari ke kokarin ya shige wani abokinsa day a wuce shi da babur. Yusuf Buhari ya gunzawa babur dinsa wuta domin ganin ya cimma abokin tsrern nasa, inda bayan tafiya kadan ya doki wani dutse a gefen titi.
An bayar da rahotannin cewar Yusuf Buhari ya buga aka, yayin da kuma ya samu kukkujewa a fuskarsa da jikinsa. Wata mata ce da ta zo wuce ta fara ganin Yusu Buhari a cewar wani makusansa.
An garzaya da Yusuf a guje zuwa asibitin Cadarcrest dake Abuja, inda anan ne yanzu haka yake karbar magani. Haka kuma, wata majiya mai tushe tace Yusuf Buhari ya bugu sosai akansa, inda aka ce har ya zuwa yanzu bai san inda kansa yake ba.