
Da alama dai yajin aikin gargaɗi da Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU ta fara ba zai kai wata ɗaya kamar yadda ta ɗauki aniya ba, bayan da Gwamnatin Nijeriya ta yi wuf ta fara yunƙurin daƙile wannan mataki na ƙungiyar.
Tuni ma dai gwamnatin, ta bakin Charles Akpan, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Labarai na Ma’aikatar Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, ya baiyana a yau Litinin a wata sanarwa.
Ya ce Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, Chris Ngige ne zai gana da shugabannin ASUU ɗin da wasu masu ruwa da tsaki a ma’aikatun gwamnati.
Ya ce za a yi ganawar ne a gobe Talata da ƙarfe 1 na rana a ofishin Ministan.