Home Labarai Yajin aiki: NLC ta baiwa gwamnatin taraiya wa’adin kwanaki 21 ta sasanta da ASUU, NASU da SSANU

Yajin aiki: NLC ta baiwa gwamnatin taraiya wa’adin kwanaki 21 ta sasanta da ASUU, NASU da SSANU

0
Yajin aiki: NLC ta baiwa gwamnatin taraiya wa’adin kwanaki 21 ta sasanta da ASUU, NASU da SSANU

 

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta shiga tsakani kan rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago na manyan makarantu da ya gurgunta harkokin jami’o’i.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta ba gwamnatin wa’adin kwanaki 21 da ta warware matsalolin da ƴaƴan Ƙungiyar Malaman jLJami’o’i, ASUU da ƙLƘungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba, NASU da kuma koken mambobin ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’in Najeriya SSANU ke yi har ma da Ƙungiyar Ƙwararru ta Ƙasa NAAT.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban NLC, Ayuba Wabba, da babban sakataren majalisar zartaswar ƙungiyar, Emmanuel Ugboaja suka sanya wa hannu ranar Larabar makon nan a Abuja.

Bayan ganawa da shugabannin kungiyoyin da abin ya shafa, Wabba ya nuna matukar damuwarsa kan yadda gwamnati ta kasa cika yarjejeniyar da ta tattaunawa da su a shekarar 2009.

Ya bayyana cewa bayan ƙarewar wa’adin kungiyar ta NLC za ta yanke hukunci kan mataki na gaba idan gwamnati ta gaza magance matsalar cikin wa’adin.