Home Labarai Yajin aiki: Shekara 11 kenan ba ai mana gyaran albashi ba — ASUU

Yajin aiki: Shekara 11 kenan ba ai mana gyaran albashi ba — ASUU

0
Yajin aiki: Shekara 11 kenan ba ai mana gyaran albashi ba — ASUU

 

 

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta ce ba a sake yin gyaran albashin malaman jami’o’in kasar nan ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Dakta Lazarus Maigoro, Shugaban kungiyar, reshen Jami’ar Jos ne ya bayyana haka a wajen zanga-zangar lumana da kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta shirya a yau Talata a Jos.

A yau din ne ƙungiyar ta NLC ta gudanar da wata zanga-zanga a fadin kasar nan domin nuna goyon bayanta ga kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin da ke da alaka da yajin aikin da jami’o’in gwamnati ke yi a Nijeriya.

Maigoro ya ce sun shiga yajin aikin ne domin neman biyan bukatunsu da kuma baiwa gwamnati damar magance matsalolin da suka ƙi ci suka ƙi cinye wa.

“Ba wai muna jin dadin yajin aikin nan ba ne, amma ya zama shine zaɓin mu kuma wannan shi ne kawai don ceto Ilimin jami’a da ya lalace a Nijeriya.

“Mun kulla yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya tun a shekarar 2009, har zuwa yau wannan yarjejeniya ba ta karbu daga hannun gwamnati ba.

“Misali, a cikin shekaru 11 da suka wuce, ba a sake duba albashin malaman jami’o’i ba. A ina a ake yin irin wannan a duniya ?

“An kafa kwamitoci don duba bukatunmu, amma gwamnati ta ki yin la’akari da shawarwarin wadannan kwamitocin,” inji shi.