Home Ilimi Yajin aikin ASUU: Ɗaliban Nijeriya sun ba da wa’adin kwanaki 9 a buɗe jami’o’in gwamnati

Yajin aikin ASUU: Ɗaliban Nijeriya sun ba da wa’adin kwanaki 9 a buɗe jami’o’in gwamnati

0
Yajin aikin ASUU: Ɗaliban Nijeriya sun ba da wa’adin kwanaki 9 a buɗe jami’o’in gwamnati

 

Kungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS reshen Kudu-maso-Gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU wa’adin kwanaki tara da a buɗe dukkanin jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasar.

Shugaban NANS na shiyyar F, Kudu Moses Onyia, ne ya bada wa’adin a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a yau Talata a Enugu.

Idan za a iya tunawa, ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargaɗi na watanni uku da wasu watanni uku.

Sanarwar ta ce ya kamata gwamnati da ASUU su yi abin da ake bukata kafin kwana tara, ta kara da cewa rashin yin hakan a cikin ko kuma a karshen wa’adin zai bar dalibai da matakin karshe na daukar wani mataki mai tsauri.

A cewar sanarwar, “daga ranar 20 zuwa 25 ga Mayu, 2022; bayan karewar wa’adin, za mu dauki matakan da za su ga daliban Najeriya na shiyyar Kudu maso Gabas a adadinsu sun toshe daya daga cikin manyan hanyoyin shiga Kudu maso Gabas – Gadar Neja.

Ya ce: “Za kuma mu toshe dukkan filayen jiragen sama guda uku da ke Kudu maso Gabas, wadanda suka hada da: filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu; Sam Mbakwe Airport, Owerri da Anambra Passenger and Cargo International Airport, Umeri, Anambra.

“Don haka, dakatar da duk wani motsi zuwa ko daga wadannan kusurwoyi na Kudu-maso-Gabas,” in ji shi.