
Ɗalibai, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS sun yi barazanar cewa za su datse duk wasu titunan gwamnatin taraiya a Jihar Oyo da ga gobe Talata idan har Ƙungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta ci gaba da yajin aiki.
Wani ɓangare na ƙungiyar da ga rukunin B ne su ka yi baraza 44nar.
Sun baiyana hakan ne yayin da su ke tsaka da zanga-zanga a sakatariyar NUJ da ke Iyangu, a Ibadan.
Ƙungiyar, wacce ta ke ƙarƙashin shugabancin Steven Tegbe ya baiwa gwamnatin taraiya da ASUU shawarar su sasanta a tsakanin su.
Ya ce babu wata bukatar a yi yajin aikin tun farko idan har za a riƙa samun fahimtar juna.
Ya nuna damuwa cewa duk sanda Gwamnati da ASUU su ka samu matsala to ɗalibai ne su ne ke shan wahala.