Home Labarai Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i da su buɗe makarantu

Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i da su buɗe makarantu

0
Yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i da su buɗe makarantu

 

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i (VCs) da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun kula da jami’o’in kasar, NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed a Abuja a yau Litinin.

Wasikar, wacce aka aika zuwa ga dukkan shugabannin jami’o’in, Dattawan jami’o’in tarayya da ciyamonin majalisun gudanarwar jami’o’in tarayya, sun yi kira gare su da su sake bude jami’o’in domin a ci gaba da karatu

“Ku tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU nan da nan suka koma/fara lakcoci; maido da ayyukan yau da kullun na jami’o’i daban-daban”, in ji wasikar.

A tuna cewa ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu domin matsa wa jami’o’in da ke neman ganin an inganta kudade, da batun albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.