Home Ilimi Yajin aikin ASUU: Kan malaman jami’ar Nassarawa ya rabu bisa umarnin koma wa bakin aiki

Yajin aikin ASUU: Kan malaman jami’ar Nassarawa ya rabu bisa umarnin koma wa bakin aiki

0
Yajin aikin ASUU: Kan malaman jami’ar Nassarawa ya rabu bisa umarnin koma wa bakin aiki

 

 

Mambobin kungiyar ASUU, reshen Jami’ar Gwamnati ta Nasarawa da ke Keffi, NSUK, sun samu rarrabuwar kai biyo bayan umarnin da mahukunta suka bayar na janye yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’in, ASUU ke ci gaba da yi.

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya amince ya biya malaman albashin su da alawus-alawus ɗin su da zarar malaman sun amince su janye yajin aikin.

Bayan haka, mahukuntan jami’ar sun amince da ranar Laraba, 28 ga watan Satumba domin ci gaba da gudanar da harkokin karatu a cibiyar.

Sai dai shugaban kungiyar ASUU, reshen NSUK, Dakta Samuel Alu, yayin da yake zantawa da manema labarai a yau Juma’a a Keffi, ya bayyana umarnin hukumar a matsayin rashin kulawa da cin amana.

Malam Alu ya dage kan cewa ba za a tilasta wa malaman su koma koyar wa ba tare da son ransu ba.

“Kungiyar ta saba da barazanar, yarfe da farfagandar da wasu ɓangarori ke yi game da gwagwarmayar.

“Ba lallai ba ne a ce muna tattaunawa da kuma cike da tsammanin masu kishin kasa za su yi wa gwagwarmayarmu zagon kasa kuma mun shirya sosai.

“Don kaucewa shakku, ASUU ɗaya ce. Don haka, bai kamata a ce ASUU a NSUK tana gudanar da ayyukanta a keɓe da sauran rassan ASUU.

“Tana aiki ne cikin cikakken bin umarnin sakatariyar kasa,” in ji shi.

Babban Rijistaran jami’ar ,Bala Ahmed ne ya fitar da sanarwar inda ya bukaci daliban su koma makaranta.