
An kammala taro tsakanin shugabannin kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU da gwamnatin tarayya ba tare da cimma matsaya ba.
Saboda haka yajin aikin da malaman jami’o’in gwamnatin ke yi na tsawon watanni shida zai ci gaba da gudana.
Malaman da suka shiga yajin aikin sun gana da kwamatin Farfesa Nimi Briggs a ranar Talata a hukumar kula da jami’o’i ta kasa da ke Abuja tare da fatan ganin an lalubo bakin zaren.
Wani jigo a Kungiyar ASUU da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa mambobin kwamitin sulhu na Briggs ba su zo da wani sabon tayi a kan teburin ba.
A maimakon haka, majiyar daga ASUU ta ce, kwamitin ya roki malaman da su dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da yin alkawarin cewa za a sanya bukatunsu a cikin kasafin kudin Shekarar 2023.
Kazalika majiyar ta ce taron wanda aka fara shi da misalin karfe 12 na Rana, an shafe kusan sa’o’i uku ba tare da cimma matsaya ba.
Kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na makonni hudu a ranar 14 ga watan Fabrairun Shekarar 2022.
Haka Kuma a ranar 14 ga Maris, kungiyar ta kara wa’adin yajin aikin zuwa wasu Karin watannin biyu domin baiwa gwamnati damar cika alkawuran da ta dauka.
An sanar da tsawaita yajin aikin zuwa makwanni 12 a ranar 9 ga watan Mayu na Shekarar 2022