Home Labarai Yajin aikin da NLC suke yi laifin Buhari ne – Mekara

Yajin aikin da NLC suke yi laifin Buhari ne – Mekara

0
Yajin aikin da NLC suke yi laifin Buhari ne – Mekara

Adamu Babale Makera mai taimakawa Gwamnan Gombe na musamman ya yi zargin cewar wannan yajin aikin da ma’aikata suke yi ba laifin kowa bane illa Shugaba Buhari. Makera ya wallafa kamar haka:

Tun kafin yajin aikin yayi nisa yana da kyau irinsu National Council of State, National Council of Traditional Rulers of Nigeria, Christian Association of Nigeria da kuma Jama’atu Nasril Islam su dauki matakan gaggawa na shigowa cikin lamarin don a kawo karshen sa saboda talakawan Najeriya zasu fuskanci matsananciyar wahala idan yajin aikin yayi tsawo. An shafe kwanaki kimanin 50 babu salari, ga kuma mugayen yan kasuwa da dillalai masu neman irin wannan dama don tsawwalawa talaka.

Ma’aikatan gwamnati a NajeRita sun chanchanci a yi musu karin albashi tun kafin zuwan Buhari, to sai dai zuwan Buhari ya kara tilasta hakan saboda wassu dalilai da dama amma zan yi tsokaci ne kawai akan guda biyu.

(1). Kamar yadda ya saba yin alkawura irin na yaudarar siyasa da kuma rashin lissafi, Buhari ya yiwa ma’aikata alkawarin zai sanar da yi musu karin albashi a karshen wannan watan da muke ciki na September, abun tambaya shine izuwa yanzu ya sanar da karin albashin da yace zai yi? Idan bai sanar ba ashe kenan ma’aikata suna da gaskiya idan suka tsunduma yajin aiki.

Batun alkawari Baba Buhari ya sha yin su amma ba ya iya cikawa, shi dai burinsa yayi muku alkawura saboda kawai ku sake zabensa a karo na biyu; to wannan alkawarin dai ga abun da ya jawo mana kuma shine ba shi da gaskiya. Rashin lissafi kuma shine ai ma’aikatan gwamnatin tarayya basu da yawa idan aka kwatantan da ma’aikatan jihohi da na kananan hukumomi, yaushe aka zauna qeqe da qeqe da shugabanni a matakin jihohi da kananan hukumomi akayi matsaya da gwamnatin tarayya cewa ga mafi karancin albashin da aka amincewa wanda jihohi da kananan hukumomi zasu iya biya? Ko a yanzu jihohi da yawa ba sa iya biyan N18,000 kuma sun gaza biyan albashi na tsawon watanni barkatai, yaushe wani zai zo musu da batun karin albashi su amince?

(2). Mu dai ba Malamai bane, to amma dole a san a ina za a ajiye mu don kuwa mu ba jahilai bane balle wani yazo yace mana wai tsadan abinci da hauhawan farashin kayayyaki daga ALLAH ne, haka kawai farashin ya tashi ba tare da dalili ba? Buhari yayi ci da zuci wajen zuwa da wassu ka’idodi irin nasa wadanda sukayi sanadiyyar hauhawan farashin kayayyaki irin wanda bamu taba gani ba a Najeriya kuma an yi ta yin kira gare shi amma yayi kememe ya ki amincewa; don haka shi muke daurawa alhakin tashin farashin kayayyaki. Kudaden da ma’aikata ke yin cefenen abinci kafin zuwan Buhari a yanzu sai sun ninka kudin sau 3, kun ga kenan karin salari ya zama dole idan yana son ma’aikatan su cigaba da rayuwa.

Alkawarin da Buhari ya yiwa ma’aikata amma ya kasa cikawa da kuma hauhawan farashin da salon mulkin sa ya jawowa yan Najeriya ne suka iza wutar wannan yajin aikin dake gudana a yanzu haka, don haka kai tsaye shine da laifi. Da fatan ALLAH YA kawo mana karshen wannan yajin aikin.